Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 02.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran

Ana cigaba da zantawa kan shirin nukiliyar Iran duk kuwa da cewar wa'adin da aka diba na kammala zaman ya kare kwanaki biyun da suka gabata.

Da ya ke tsokaci kan wannan batu, ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce suna fatan ganin an amince da yarjejeniya da za ta kasance marar gibi a cikinta.

Steinmeier ya ce ''sakamakon da tattaunawar nan zai haifar abu ne da zai shafi kusan kowa musamman ma kasashen da ke makotaka da Iran don haka ya kamata mu amince da yarjejeniya da za ta kasance ba ta da wata matsala.''

Shirin nukiliyar Iran dai na shan suka daga kasashen duniya inda suke zargin ta na yin sa da nufin samar da makamin kare dangi, zargin da Iran din ta sha musantawa inda ta kan ce shirin na ta na zaman lafiya ne.