Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 09.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran

Hukumar da ke sanya idanu kan makashin nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato IAEA ta ce Iran za ta koma kan taburin tattaunawa da jami'anta a cikin watan gobe.

Kakakin hukumar ta IAEA Gill Tudor ta ce maƙasudin tatattunawar ita ce warware matsalar da a baya su ka fuskanta ta gaza kaiwa ga cibiyoyin nukilyar Iran ɗin domin gudanar da bincike biyo bayan ganowar da ta ce hukumar ta yi na yunƙurin Tehran ɗin na wuce gona da iri a shirin na su na nukiliya.

Wannan tattaunawar dai na zuwa ne kimanin watanni huɗu bayan gaza cimma wani abu na a zo a gani da Iran ɗin da hukumar su ka yi a baya dangane da shirin na ta na nukilya wanda Isra'la da Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya ke ganin wani yunƙuri ne na mallakar makaman ƙare dangi, zargin da Iran ɗin ta sha musantawa inda ta ce shirin na ta na zaman lafiya ne.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi