Tattaunawa kan rikicin Yemen | Labarai | DW | 30.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan rikicin Yemen

Sarki Salman na Saudi Arabiya ya ce kasarsa a shirye ta ke ta tattauna da jam'iyyun siyasar kasar Yemen da ke son ganin zaman lafiya ya wanzu a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Saudi din ya ce Sarki Salman na son ganin wannan tattaunawa ta gudana karkashin wata gamayya ta kasashen yankin Gulf, kana ya ce sharudan tattaunawar sun hada da maidawa gwamnati makaman da ke hannun 'yan tawaye da kuma tabbatar da zaman lafiyar kasashen da ke makotaka da Yemen.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Saudi Arabiya din da wasu kasashen na yankin ke yin luguden wuta kan 'yan kungiyar ta Houthi mabiya tafarkin shi'a da ke son karbe iko, har aka bada labarin rasuwar mutane 21 daidai lokacin da wani roka ya afkawa wani sansani na 'yan gudun hijira a kasar.