Tattaunawa domin magance rikicin Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 06.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa domin magance rikicin Sudan ta Kudu

An fara tattaunawa ta gaba da gaba tsakanin bangarorin da ke rikici a Sudan ta Kudu

A birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, an fara tattaunawa ta gaba da gaba tsakanin bangarorin da ke rikici na Juba a kasar Sudan ta Kudu, domin shawo kan rikicin na makonni uku. Masu shiga tsakani sun ce har yanzu akwai sauran aiki bisa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya kai ziyara zuwa Juba babban birnin kasar ta Sudan ta Kudu, inda ya gana da Shugaba Salva Kiir kan hanyoyin da za a magance matsalar. Shugabannin sun yi magana kan dakarun hadin gwiwa da za su kare wuraren hakar man fetur da kasashen ke samun kudaden shiga.

Kasar ta Sudan ta Kudu ta fada cikin sabon rikici a ranar 15 ga watan jiya na Disamba, abin da ya janyo mutuwar fiye da mutane dubu, sannan wasu dubu 200 suka tsere daga gidajensu. Yanzu haka ana ci gaba da samun tashin hankali, duk da zaman tattaunawar da ke gudana a birnin na Addis Ababa.

Shekaru biyu da suka gabata, wato a shekara ta 2011 ne Sudan ta Kudu ta balle daga cikin kasar Sudan, bayan yakin basasa na dogon lokaci, kuma yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara ta 2005 ta taimaka wa kasar ballewa cikin sauki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh