1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa a kan rikicin nukiliyar Iran

October 15, 2013

Manyan kasashe da ke fada a ji a duniya ciki har da Jamus na nazarin shawarwarin da Iran ta gabatar game da shirinta na nukiliya da aka yi ta kai ruwa rana akai.

https://p.dw.com/p/1A0O4
Hoto: Reuters

Kasar Iran ta fara tattaunawa da kasashen nan biyar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus a kan shirinta na nukiliya da aka dade ana takaddama akai. Tawagar ta jami'an gwamnatin Teheran ta gabatar da shawarwari da za su kai bangarorin biyu ga cimma matsaya game da wannan batu yayin tattaunawar ta kwanaki biyu a birnin Geneva. Sai dai har yanzu hanyu ba a bayyana abubuwan da shawarwarin na Iran suka kunsa ba.

Daga cikin wadanda suke halartar tattaunawar har da kantomar harkokin waje ta Kungiyar Gamayyar Turai Catherine Ashton da ku ministan harkokin wajen Iran Mohammad Jawad Zarif. Wannan tattaunawar ita ce ta farko da aka shirya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya tun bayan da Hassan Rohani da ke da matsakaicin ra'ayin rikau ya dare kan kujerar mulkin Iran. kasashen yammacin duniya suna danganta wannan keke da keken da zakaran gwajin dafi na kokarin da shugaba Rohani ya yi alkawarin yi na magance takaddamar nukilyar kasarsa wato Iran.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal