1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a tafka asara a sakamakon sauyin yanayi

Ramatu Garba Baba
November 20, 2019

Binciken masana ya gano yadda matsaloli daga sauyin yanayi za su iya janyo wa duniya asarar fiye da dala triliysn bakwai a sakamakon karuwar ambaliya da fari da kuma karancin abinci.

https://p.dw.com/p/3TMUE
Banknoten von verschiedenen Währungen
Hoto: picture-alliance/dpa/Q. Shen

Hasashen na cewa karuwar fari da ambaliya da kuma rashin wadatar amfanin gona sun kasance barazanar da ake fuskanta da ka iya durkusar da tattalin arzikin kasashen duniya da dama. Kiyasin na nuni da cewa, akwai yiyuwar samun asarar dala Triliyon 7.9 nan da shekarar 2050.

Sakamakon binciken na wannan Laraba da yayi nazari kan kasashe akalla tamanin da biyu, ya gano nahiyar Afrika ke sahun gaba inda ta kasance cikin hadari, amma kuma kasar Rasha na matakin farko daga cikin kasashen duniya da za ta fi fuskantar matsalar. A Afirka, matsalar za ta fi shafar kasar Angola ta la'akari da karfin tattalin arzikinta da ya dogara kacokan a kan noma sai kuma Najeriya da Masar da Bangladesh da kuma Venezuela da ke fuskantar barazanar a cewar binciken.