Tasirin gwamnatin hadin kan kasa a Libiya | Siyasa | DW | 19.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tasirin gwamnatin hadin kan kasa a Libiya

Bayan zazzafar mahawarar da suka yi kwanaki suna yi, daga karshe dai bangarori biyu masu rikici a Libiya sun cimma kafa gwamnatin hadin kan kasa da zai kawar da tagwayen gwamnatoci.

An yi ta rera taken Allah ja zamanin kasar Libiya a matsayinta na kasa daya dunkulalliya, mai dauwamman kwanciyar hankali da zaman lafiya da bunkasa mai dorewa.Taken da Muhammad Mugari ,jagoran zaman taron ya ce, dama su kansu dashi sukai la,akari wajen kafa wannan sabuwar gwamnatin:

"Da ma takenmu a yayin ganawarmu shi ne, samar da dunkulalliyar kasar Libiya karkashin jagoranci daya.Kuma Allah ya taimaka mun cimma hakan. Al,ummar Libiya,dama sauran kasashen duniya, zasu san cewa, wannan ita ce nagartacciyar hanya ta salama da muka yi gamo da katar wajen binta."

Flüchtlinge in Lybien

'Yan gudun hijira

Gwamnatin hadin kan kasar da hamshakin attajiri nan Fayez al-Sarraj ke jagoranta,wacca ta kunshi ministoci 32, zata fara gudanar da aikinta daga tsohuwar fadar mulkin kasar da 'Yan tawaye ke rike da ita watauTripoli, da zarar majalisar dokokin kasar da duniya ta amince da ita da ke birnin Tubruq ta amince da ita nan da kwanaki goma.

Ahmad Suraj,shi ne sabon ministan yada labarai a gwamnatin hadin kan kasar da ke jiran samun cikakken halacci, ya fadi manyan kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin:

"Daga yauzu mun bude sabon shafi na fafutukar gina kasa, da sasantawa da yafar juna. Mun kama hanyar sake gina kasa da farfado da tattalin arzikinta da mayar da wadanda yaki ya daidaita zuwa gidajensu. Mun kama hanyar kafa dunkulalliyar rundunar sojin da bata biyayya ga kowa face ga al,ummar Libiya ta hanyar raba su da 'yan ta,adda da miyagu da kare kasa daga duk wata barazana. Mun kama hanyar daukar duk matakan da suka wajaba don warware matsalolinmu."

Libyen Armee Helikopter

Jirgi kirar saukar ungulu na mayakan Libiya

Mai shiga tsakani na MDD a rikicin kasar ta Libiya, Martin Kobler ,a wani sakon da ya tura a shafinsa na twitter, ya taya 'yan kasar murna kan abin da ya kira" gagarumar nasarar da suka yi wacca ta shiga kundin tarihi" , yana mai kira ga amintacciyar majalisar kasar data gaggauta amincewa da hukumar hadin kan kasar.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne dai, bangarori biyun da ke fafatawa da juna tun bayan kifar da Kanal Gaddafi shekaru biyar din da suka gabata, suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a garin Sukairat na kasar Maroko, wacca ta tanadi dakatar da yaki da kafa gwamnatin hadaka, matakin da ya samu yabo da jinjina daga kasashen duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin