Tashin bama - bamai a Uganda | Labarai | DW | 12.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bama - bamai a Uganda

'Yan kallon gasar ƙwallon ƙafar Duniya 64 ne suka mutu bayan tashin bam a Uganda

default

Aƙalla mutane 64 ne suka mutu sakamakon tarwatsewar bama - bamai a wasu gidajen cin abinci biyu da ke Kampala babban birnin ƙasar Uganda. Jami'an 'yan sanda suka ce ɗaya ga cikin bama - baman ya tashi ne a wani gidan cin abinci na 'yan ƙasar Ethiopia dake kudancin birnin na Kampala, a yayin da guda kuma ya fashe a wajen sha'ƙatawar 'yan wasan zari - ruga da ke gabashin birnin na Kampala. Tagwayen bama - baman sun tarwatse ne sa'adda mutane ke kallon gasar ƙarshe ta ƙwallon ƙafar cin kofin Duniyar da Afirka ta kudu ke karɓar baƙunci ta na'urar telebijin.

Ofishin jakadancin ƙasar Amirka ya tabbatar da cewar akwai wani ba-Amirke cikin waɗanda matsalar ta rutsa da su. Ko da shike ya zuwa yanzu ba'a kaiga sanin manufar ƙaddamar da harin ba, amma mayaƙan sa kai na ƙasar Somaliya sun yi barazanar ƙaddamar da hare - hare a birnin Kampala - a matsayin hanyar nuna rashin jin daɗin su ga dakarun da Uganda ta tura Mogadishu, babban birnin ƙasar Somalia.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed