Tashe-tashen hankulla a Irak | Labarai | DW | 08.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe-tashen hankulla a Irak

A ci gaba da tashen tashen hankulla a ƙasar Irak, mutane 24 su ka rasa rayuka yau, a birnin Bagadaza.

Yan ƙunar baƙin wake sun kai hare -haren bama bamai ,a waurare 5, daban-daban na birnin.

Wannan hare hare, sun wakana a lokacin da, ƙarin sojoji kussan dubu 4, na Amurika,ke shirin zuwa Bagadaza, domin fuskantar yan yaƙin sunƙuru.

Praminista Nuri Al Maliki, ya yi Allah wadai ,ga dakarun Amurika, a sakamakon wasu hare hare da su ka kai a birnin Sadr City.

Praministan ya ce, an kai wannan samame tsakanin daren lahadi zuwa litinin ,da burin fattatakar yan shi´a,ba tare da izinin sa ba.

A tsawan sa´o´i da dama, an yi ɓarin wuta, tsakanin dakarun Moqtada Sadr, da sojojin Amurika.

A ɗaya wajen kuma, an gano gawawakin sojojinIraki 7 da su ka rasa rayuka kussan dac iyaka da Iran.

Ita kuwa rundunar sojan Amurika, ta bayana mutuwar sojan ta ɗaya, a yankin Al Anbar.

Daga farkon yaƙin Irak zuwa yanzu ,baki ɗaya sojoji 2.591 na Amurika su ka sheƙa lahira.