1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankula na kawo cikas ga tallafa wa Libiya

March 6, 2014

A wani taro wani taron ministocin harkokin wajen kasashen yamma a birnin Rome, Italiya ta yi gargadin cewa rashin tsaro a Libiya na kawo tseko ga aikin tallafa wa kasar.

https://p.dw.com/p/1BLSU
Unruhen in Libyen 02. März 2014
Hoto: MAHMUD TURKIA/AFP/Getty Images

Sabuwar ministar harkokin wajen Italiya Federica Mogherini ta ce rashin kwanciyar hankalin siyasa a Libiya na kawo cikas ga kokarin kasashen duniya na ba da tallafi ga kasar mai fama da rarrabuwar kawuna. Mogherini ta fada wa firaministan Libiya Ali Zeidan da kuma wata tawagar ministocin harkokin waje kasashen yamma da ke wani taro a birnin Rome cewa a shirye kawayen Libiya na kasa da kasa suke su taimaka wa Libiya, amma bazuwar makamai babu iyaka a cikin kasar na kawo babban cikas. Taron na birnin Rome da ya samu halartar sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, da ministan harkokin wajen Jamus Walter Steinmeier ya duba irin taimakon da za a ba wa gwamnatin rikon kwaryar Libiya tare da nazarin karin taimakon da za a ba wa kasar ta Libiya saboda gaskiyar cewa wasu kungiyoyin 'yan ta'adda sun fara hada kai a kudancin kasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal