1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Mogadishu

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 20, 2007

Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu fiye da 45 kuma suka samu raunuka cikin fada mafi muni a birnin Mogadishu tun bayanda dakarun Habasha suka shiga kasar Somalia a watan Disamban bara

https://p.dw.com/p/Btw9
Hoto: AP

Wasu yan bindiga ne dai suka kai hari a birnin na Mogadishu suna masu maida martani game da wani hari da dakarun Hbasha suka kai da manyan rokoki inda suka halaka fararen hula 5 a kasuwar Bakara dake cikin birnin.

Jamian gwamnati sun sanarda da cewa wani fada ya sake tashi yayinda wasu yan bindigar kuma suka kai hari kan fadar shugaban kasa da kuma bakin ruwa inda dukkaninsu sansanoni ne na dakarun Habasha.

Shugaban sashen gaugawa na asibitin Madina dake birnin Mogadishu Abdi aden Abdulle yace sun karbi kimanin mutane 36 da suka samu raunuka,sai dai kuma babu isassun kayan aiki da zasu kula da su.

A karshen shekara data gabata hare hare a birnin Mogadishu sun tilastawa daruruwan jamaa tserewa zuwa yankunan karkara wadanda har yanzu gwamnati bata kame su,domin tsira da ransu.Da dama kuma sun halaka cikin wadannan hare hare.

Wani jamiin gwamnatin kasar da ya nemi a boye sunansa ya sanarda da cewa wasu sojojin Habasha biyu sun rasa rayukansu lokacinda wani gurneti ya fada fadar shugaban kasa,sai dai mataimakin ministan tsaro Salad Ali Jelle ya karyata wannan rahoto,hakazalika yace dakarun gwamnati dana Habasha basu harba koda harsashe daya ba.

Birnin Mogadishu dai yana fama da rashin tsaro tun bayan korar shugabanin kotunan musulunci wadanda suka maido da doka da oda cikin birnin na kusan tsawon watanni 6.

Gwamnati kuma a nata bangare tana ta kokarin tabbatar da ikonta a kasar tun korar mayakan na islama tare da taimakon dakarun Habasha wadanda suke jiran isowar dakarun AU kafin su kwashe yanasu yanasu su bar kasar.

Kasar Somalia dai ta fada cikin halin kaka nikayi net un hambarar da shugaban kama karya Muhammad Siad Barre a 1991.

A halinda ake ciki kuma maaikatar harkokin wajen kasae Sweden tace an tsare wasu yan kasarta 4 a kasar ta Somalia bisa zargin yin fada kafada da kafada da mayakan islama.

Kakakin maaikatar Andre Mkandwire yace har yanzu maaikatar tana kokarin gano inda wadannan mutane suke tsare.

Ya kuma baiyana cewa 3 daga cikinsu yan asalin kasar ta Sweden ne yayinda na hudun yake dauke da takaradar iznin zama dan kasa,kodayake ab dauke shi a matsayin dan asalin kasar.

Tuni dai ake ta yada jita jitar cewa an tsare yan kasar ta Sweden a Somalia