Tashar Al-Jazeera ta yi tir da rufe ofishinta da Isra′ila ta yi | Labarai | DW | 07.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashar Al-Jazeera ta yi tir da rufe ofishinta da Isra'ila ta yi

Matakin da Isra'ila ta dauka ya biyo bayan matakan da wasu kasashen Larabawa hudu suka dauka a kan kasar Katar mai mallakar tashar ta Al-Jazeera, inda suka zarge ta da mara wa ayyukan ta'addanci baya.

Al-Jazeera in Jerusalem (picture-alliance/abaca)

Ofishin Al-Jazeera a Birnin Kudus

A wannan Litinin tashar talabijin ta Al-Jazeera ta yi tir da matakin da Isra'ila ta dauka na rufe ofishinta da ke Birnin Kudus, tana mai cewa matakin ya saba wa demokuradiyya, ta ce za ta dauki mataki na shari'a.

Matakin da Isra'ila ta dauka ya biyo bayan matakan da wasu kasashen Larabawa hudu suka dauka ne a kan kasar Katar mai mallakar tashar ta Al-Jazeera, inda suka zarge ta da mara wa ayyukan ta'addanci baya.

Isra'ila dai ta jima tana zargin tashar da nuna mata bambanci da angiza mutane su ta da zaune tsaye a labaran da take watsawa.

Sai dai 'yan Isra'ila na da ra'ayi mabambanta dangane da rufe ofishin tashar a Birnin Kudus, yayin da wasu ke maraba da matakin wasu kuwa cewa suka yi bai dace ba, kamar yadda wannan mazaunin Birnin Kudus ya nunar.

Ya ce: "Matukar muna son mu zauna a cikin wata kasa ta demokuradiyya to ba daidai ba ne hukuma ta sanya takunkumi kan wata kafar yada labaru. Ba ruwana da inda ta fito, idan suna nan kan wata yarjejeniya, suna da kuma izinin yin aiki a Isra'ila, ai za su iya bayyana ra'ayin da suke so. Ko da yake ni kai na ba na son Al-Jazeera."