Taron yan adawan Somalia a Eritrea | Labarai | DW | 06.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron yan adawan Somalia a Eritrea

Shugaban gamayyar kotunan musulmi na Soimalia Sheikh Hassan Dahir Aweya,wanda ya bace tun bayan fadan daya kori mayakansa daga kudancin somalia a karshen shekarar data gabata,ya bayyana a taron yan adawa dake gudana a kasar Eritrea ,yau.Jagorar kungiyar musulmin ,wanda ake zargi da hare haren da ake kaiwa dakarun gwamnati a mohadsishu,yana daya daga cikin manyan mahalarta taron jamiiyyun adawan na somalia a wani dakin taro a birnin Asmara.A jawabinsa a wurin taron tsohon kakakin majalisar,wanda kuma ke zama tsohon ministan harkokin cikin gida na Somalia,Shekh Sharif Ahmed,yayi kira ga Amurka data hada kai da yan adawa na Somalian,tare da watsi da zargin tarzoma da Habasha take musu.Taron wanda ya samu halartan wakilai 300 da suka hadar da wakilan mdd da faransa da izraela da kungiyara Eu,ya bukaci Amurkan da ta dada taka muhimmiyar rawa cikin warware rikicin kasar.