Taron yaki da ta′addanci a Afirka ta yamma | Labarai | DW | 10.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron yaki da ta'addanci a Afirka ta yamma

Babban Magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa rundunar G5 Sahel ba ta da kafin da za ta iya kawar da kungiyoyin 'yan ta'adda a yakin yammacin Afirka ita kadai. 

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana hakan ne a wannan Laraba a jawabin bude babban taron yaki da ta'addanci a Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya inda ya ce wannan matsala ta faro daga kasar Mali ta yadu zuwa kasashen Nijar da burkina Faso, da kuma sannu a hankali ke yaduwa zuwa kasashen Ghana da Togo da Cote d'Ivoire. 

Sai dai Guterres a shirye yake ya kawo goyon bayansa ga duk wani shiri da shugabannin nahiyar za su fito da shi na yakar ta'addanci a nahiyar baki daya. Guterres ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya kasa sanya kungiyar ta G5 Sahel a karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda kasashe mambobin kungiyar suka bukata sau tari.