Taron WTO a Kenya ya haure lokaci | Labarai | DW | 18.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron WTO a Kenya ya haure lokaci

A kwai takaddama a taron na Nairobi kan batun kawar da tallafi a kasuwancin kayan amfanin gona da ake fitarwa zuwa kasashen ketare.

Kenia WTO-Konferenz

Mahalarta taron WTO a Kenya

Alamu na nuni da cewa tattaunawar da ake yi tsakanin ministocin kasuwanci daga kasashe masu tasowa da masu karfin tattalin arziki a Nairobin Kenya karkashin kungiyar kasuwanci ta WTO sai an kai ga karin lokaci bayan da aka gaza cimma matsaya ta karshe a ranar Juma'an nan. Duk da irin tattaunawar da aka yi tsawon daren jiya Alhamis masu hahalarta taron sun gaza wajen cimma matsaya ta bai daya da za ta sanya a kammala taron a ranar Juma'an nan kamar yadda aka tsara.

Kasashe masu tasowa na bukatar ganin mambobin kungiyar ta WTO sun tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Doha a 2001, wacce za ta sanya a yi kasuwanci tsakanin kasashe masu kudi da matalauta ba tare da shinge ba.

Kasar China da Indiya da arzikinsu ke bunkasa dai ana ganin su za su fi cin moriyar shirin na musamman, kasancewar sanya su cikin masu tasowa, yayin da kasashe irin na Amirka da na Turai suka sa himma wajen ganin an samar da mafita ga harkokin kasuwanci na bai daya a duniya da suka hadar da harkokin zuba jari da kasuwanci a shafukan intanet da ma hanyoyi sarrafa kayayyaki da kasashen ke samarwa.

Har ila yau akwai takaddama a taron na Nairobi kan batun kawar da tallafi a kasuwancin kayan amfanin gona da ake fitarwa zuwa kasashen ketare.