Taron shugabannin kasashen yankin Pacifik da Asia a Sydney | Labarai | DW | 07.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabannin kasashen yankin Pacifik da Asia a Sydney

Kasashen dake yankin pacifik sun cimma sun cimma matsaya guda dangane da batutuwan da suka shafi dumamar yanayi,wanda ya kawo karshen sabanin dake tsakanin kasashe masu cigaban masana’antu da matalauta.Kwararru daga wakilan kasashe 21 dake kungiyar tattali na kasashen yankin Asia da Pacifik ne ,suka cimma yarjejeniya kann batun Dumamar yanayin ,wanda kuma ake saran gabatarwa shugabannin kasashen dake halartan taron da zaa bude a gobe Asabar.Idan har wannan yarjejeniya ta samu amincewa a wannan taro,zai kasance gagarumar nasara wa Amurka da Australia,na samun amincewar China ,dake zama daya daga cikin kasashen duniya dake haifar da barazanar iskar gas mai guba da masanaantu ke fitarwa,da kuma wasu kasashe masu tasowa ,yin alkawarin taimakawa shawo kann matsalar.