Taron shugabannin kasashen Kungiyar IGAD | Labarai | DW | 04.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabannin kasashen Kungiyar IGAD

Shugabannin kasashe na yankin Gabashin Afirka na Kungiyar IGAD za su gudanar da wani taro a gobe Juma'a a birnin Addis Ababa na Habasha domin tattauna rikicin Sudan ta Kudu.

An shirya shugabannin za su tattauna batun tura wata runduna ta musammun a Sudan ta Kudu domin tabbartar da zaman lafiya, bayan tashin hankali na baya-baya nan da ya barke a kasar tsakanin dakarun gwamnatrin na Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.Tun a shekara ta 2013 kasar ta Sudan ta Kudu take fama da yaki basassa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar gomai na dubban rayukan jama'a