1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin yanayi kalubalen duniya

Yusuf Bala Nayaya
December 14, 2018

A wannan rana ta Juma'a ce ake kammala taron sauyin yanayi bayan makonni biyu ana tafka muhawara wacce har yanzu akwai muhimman batutuwa da aka gaza warwarewa.

https://p.dw.com/p/3A5Tn
UN-Klimakonferenz 2018 in Katowice, Polen | Gruppenbild
Hoto: picture-alliance/dpa/Keystone/P. Klaunzer

Masu tattaunawar daga kasashe 196 na duniya sun sake kashe daren Alhamis wayewar garin Juma'a a birnin Katowice na Poland a kokari na ganin an samu ci gaba wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a birnin Paris a shekara ta 2015, mai kudiri na rage dumamar da duniya ke yi na kasa da digiri biyu a ma'aunin Celsius.

Ana dai ci gaba da fuskantar gwama numfashi a taron na Katowice kan batun kudin da za a kashe wajen tunkarar matsalar ta sauyin yanayi inda kasashe marasa karfi wadanda illar ta sauyin yanayi ta fi tagayyarawa ke neman kari na kudade daga kasashe masu arziki kan aikace-aikace na rage radadin sauyin na yanayi. Abin da ke zuwa bayan da masu bincike suka gano karuwar fitar da iskar ta Carbon mai gurbata muhalli a shekarar 2018 da kashi biyu cikin dari. Haka wasu kungiyoyi na MDD na nuna shakku kan mayar da hankali na kasashe wajen rage dumamar da duniyar ke yi kasa da digiri biyu kamar yadda ake muradi a yarjejeniyar ta Paris.