Taron ministocin tsaro na kasashen Sahel | Labarai | DW | 15.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin tsaro na kasashen Sahel

A wannan Litinin din ministocin tsaro daga kasashe biyar na yankin Sahel suka gudanar da wani taro a birnin Paris a wani yunkuri na girke rundunar yaki da ta'addanci ta G5 Sahel a yankin.

Gipfeltreffen in Bamako Mali (Reuters/C. Archambault)

Shugabannin kasashe biya na G5 Sahel tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron

Yunkurin na magance ta'addanci da sauran muggan laifuka ya hada kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Jamhuriyar Nijar wadanda zasu hada gwiwa don kirkirar wata rundunar tsaro mai dakaru 5000 kafin tsakiyar shekarar 2018 don magance ta'addanci da dangoginsa a yankin.

Wadannan kasashe sun yi fama da hare-haren da suka samo asali daga Najeriya wanda ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka tare da raba mutane da muhallansu abinda yayi sandaiyyar gurgunta tattalin arzikin kasar da kuma haifar da matsananciyar yunwa.

Rundunar ta G5 Sahel ana sa ran za ta yi aiki tare da dakarun Faransa da kuma Jami'an kwantar da tarzoma dubu 12 na MINUSMA da ke aiki a kasar Mali.