Taron koli na Afirka da Faransa a Mali | Labarai | DW | 13.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron koli na Afirka da Faransa a Mali

Shugabanni daga kasashe 30 da Faransa na taron koli na dangantakar kasashen nahiyar Afirka da Faransa a birnin Bamako na Kasar Mali karkashin jagorancin Shugaba Hollade na Faransa.

Francois Hollande spricht zur feierlichen Amtseinführung Keitas in Mali (Reuters/Michel Euler)

Shugaba Hollande na Faransa da Shugaba Keita na Mali

Taron dai ana sa ran zai mayar da hankali kan yaki da masu ikirarin Jihadi da inganta dimokradiya. Har ila yau a wani bangare na taron, ministocin harkokin kasashen wajen wadannan kasashe za su yi wani zama a gobe Asabar inda za su duba batun 'yan gudun hijira kamar yadda wadanda suka shirya taron Faransa da Mali suka bayyana.

Mafi yawa daga cikin kasashen da ke halartar taron na zama wadanda Faransa ta taba yi musu mulkin mallaka, akwai kuma wadanda ke magana da harshen Ingilishi. Faransa dai tun bayan taron shekarar 2013 ta na bada horon soji ga fiye da sojojin Afirka 20,000 a kowace shekarakamar yadda majiyar jami'an diplomasiyar Fransa ke fadi. Adadin kuma da a fadar majiyar zai kai daga yanzu 25,000 a kowace shekara.