Taron koli kan tsaro a Dakar | Siyasa | DW | 16.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron koli kan tsaro a Dakar

Shugabannin kasashen Afirka da abokan huldarsu na kasa da kasa, na halartar zaman taron kwanaki biyu kan batun zaman lafiya a yankin Sahel da ke gudana Senegal.

Shugabannin kasashen Afirka tare da abokan huldarsu na kasa da kasa, na halartar wani babban zaman taro kwanaki biyu kan batun zaman lafiya a yankin Sahel da ke gudana a birnin Dakar na kasar Senegal. Wannan zaman taro dai zai yi kokarin samar da hanyoyin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a wannan bangare na Afirka, kuma ganin mahimmancin wannan haduwa, kowa ya zuba idanu ya ga sakamakon da wannan taro zai haifar.

Wannan babban zaman taro ya hada manyan masana harkokin tsaro na Afirka, inda suke kokarin zurfafa tunaninsu domin fitar da wasu dabaru tsakanin kasashen na Afirka da ma kasashen duniya da ke mara musu baya kan wannan batu don ganin an fuskanci barazanar 'yan ta'adda masu tada kayar baya a yankin na Sahel, kuma wannan ne ya sanya daga ko'ina, ake jiran babban sakamako daga wannan taro. Amma kuma a cewar Pathé Mbodji, dan jarida, kuma mai sharhi kan al'ammuran siyasar Afirka, samun mafita ga matsalolin tsaron da kasashen na Afirka ke fuskanta, na iya samuwa ne ta hanyar hada karfi da gaskiya tsakanin kasashen musamman ma masu makwabtaka da inda aka fi samun matsalolin.

" Haduwa ce wadda 'yan Afirka tsakaninsu da sauran abokan huldarsu zasu tattauna domin ganin sun saka wani tsari na bai-daya da zai basu damar kawar da wadannan matsaloli na tsaro, musamman idan aka kafa wata rundunar hadin gwiwa ta gaggawa. Sannan kuma zasu dukufa ne wajen samar da mafita kan batun ta'addanci a yankin Sahel da Sahara."

Batutuwa da dama ne dai ake tattaunawa kansu yayin wannan zaman taro na kwanaki biyu, wadanda suka hada da batun warware duk wani rikici, da yaki da ta'addanci, da kuma martani ta hanyar soja da ma fararan hula kan duk wasu matsaloli da suka shafi nahiyar ta Afirka. A cewar Cheikh Tidiane, tsofon ministan harkokin wajan kasar Senegal, kuma daya daga cikin masu ruwa da tsaki kan wannan taro, lalle 'yan Afirka na bukatar cikakken hadin gwiwa idan suna son fuskantar wannan kalubane.

"A samu gano dukkan illahirin wuraren da ke da barazana a yankin Sahel da Sahara na nahiyar Afirka lalle babban aiki ne, ni a gani na yana da kyau a ci gaba da aiki tare ana tattaunawa, kuma ni nawa ganin shi ne kawai kasashen Afirka su sa hannu cikin aljihunansu tare da sanin kalubanan da ke gaban su na tsaro"

Soldaten der malischen Armee bei einer Übung

Sojojin Mali suna atisaye

Sai dai daga nashi bangare dan jarida kuma mai sharhi kan harkokin siyasa a Afirka Pathé Mbodji, ya kara nanata batunsa na ganin kasashen na Afirka sun fitar da shawarwari na gari masu inganci.

"A hakikanin gaskiya sai fa 'yan Afirka sun fito karara sun sanar da jama'arsu cewa ga hanyoyi takamaimai na samun mafita, kuma yana da kyau a ce Afirka tayi kokarin kwatanta wani kokari nata na kanta wajan magance matsalolinta."

Wannan babban zaman taro dai na birnin Dakar na samun halartar shugabannin kasashen yankin Sahel da suka hada da Ibrahima Boubacar Keita na kasar Mali, da Mohamed Ould Abdel Aziz, na kasar Mauritaniya, da Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, da Idriss Deby Itno na kasar Chadi.

Da ya ke magana yayin wannan taro kan zaman lafiya a yankin na Sahel, ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, ya yi kira ga Najeriya da sauran kasashe makwabtanta da suka kara hada karfi wajen yakar 'yan kungiyar Boko Haram da ke ci gaba ta tayar da kayar baya a kasar ta Najeriya, tare da kasancewa babbar barazana ga sauran kasashen na Sahel inda kasar ta Faransa ta ce a shirye ta ke ta bada gudunmowa ta manyan sojojinta da zasu tallafawa rundunar hadin gwiwa ta kasashe makwabtan na Najeriya dan cimma nassara.

Sauti da bidiyo akan labarin