Taron gaggawa kan Aleppo na Siriya | Labarai | DW | 18.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron gaggawa kan Aleppo na Siriya

Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da wani taron gaggawa na musamman dangane da halin taskun da fararen hula ke ciki a birnin Aleppo na Siriya.

Syrien Krieg Kämpfe in Aleppo (Getty Images/AFP/A. Alhalbi)

Hare-haren Aleppo na barazana ga fararen hula

Wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar, ta nunar da cewa taron zai gudana ne a ranar Jumma'a 21 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki, biyo bayan bukatar hakan da Birtaniya ta yi. Kungiyar kawayen Siriya da ta kunshi kasashe 11, daga kasashen Larabawa da kuma Amirka da Birtaniya wadanda kuma ke goyon bayan 'yan tawayen Siriyan ne, suka gabatar da wannan bukata ga ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva.