1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kasashe masu karfin tattalin arziki

Ramatu Garba Baba
November 14, 2022

Shugaban Amirka Joe Biden da takwaransa na Chaina Xi Jinping sun gana a tsibirin Bali na kasar Indonesiya a gabanin babban taron koli na kasashe masu karfin tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/4JV7t
Shugaba Xi Jinping da takwaransa Joe BidenHoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Shugabanin kasashe masu karfin tattalin arziki da dama sun isa tsibirin Bali da ke kasar Indonesiya don halatar taron koli na G20 kuma tuni Shugaba Joe Biden na Amirka da takwaransa na Chaina Xi Jinping suka yi wata ganawa, wace ita ce ta farko ta keke da keke tun bayan da Biden ya hau karagar mulki, ana sa ran za su yi kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu a yayin wannan ganawar da suka yi a gefen taron na G20 a wannan Litinin.

A hukumance daga gobe Talata za a soma taron kuma halin da duniya ta tsinci kai na tashin farashin kayayyaki da tsadar makamashi a sakamakon yakin Rasha da Ukraine, za su kasance daga cikin manyan batutuwan da shugabanin za su tattauna a taron, babu alama Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai halarci taron a sakamakon yadda aka mayar da kasar saniyar ware saboda mamayar Ukraine.