Taron duniya kan sauyin yanayi a Poland | Zamantakewa | DW | 13.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taron duniya kan sauyin yanayi a Poland

Shugabannin kasashen duniya sun jaddada kudirin yaki da sauyin yanayi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayin a birnin Katowice na kasar Poland.

Kasashe kusan 200 da suka hallara a birnin Katowice a kasar Poland sun amince cewar duniya na fuskantar barazana mai girma, kuma akwai bukatar daukar matakan gaggawa na tunkarar matsalar sauyin yanayin da ke yin barazana a ko ina.

Babban burin mahalarta taron shi ne samar da dabarun rage yawan amfani da sinadarin Carbon da kusan kaso 45 nan da shekaru 12 da ke tafe sannan kuma da kai karshensa gaba daya zuwa shekara ta 2050.

Duniyar dai na fatan karkata zuwa ga makamashi mara gurbata muhalli kamar hasken rana duk a cikin neman mafitar kare dumamar da ke zaman barazana mai girman gaske a cewar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres.

Sauti da bidiyo akan labarin