Taron AU karo na 30 ya cimma matsaya kan wasu batutuwa
February 1, 2018Talla
Taron koli na Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU karo na 30 da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya mayar da hankali kan batutuwa da ke ci wa nahiyar tuwo a kwarya a halin yanzu da suka hada da matsalar karancin kudin gudanarwar kungiyar, da ta 'yan gudun hijira da kuma ta yake-yake da rigingimun siyasar da ake fama da su a wasu kasashen nahiyar. Kazalika taron ya duba batun yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar kana ya amince da wasu matakai kan inganta sufurin jiragen sama a nahiyar da dai sauran batutuwa.