Taro tsakanin Hamas da Fatah a Gaza | Labarai | DW | 09.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taro tsakanin Hamas da Fatah a Gaza

Nan gaba a yau ne, a ke komawa tebrin shawara, tsakanin ƙungiyar Hamas, da jam´iyar Fatah, domin ci gaba da tunanin girka sabuwar gwamnati a Palestinu.

Tun jiya, ta kamata a fara wannan haɗuwa, amma a ka ɗage ta zuwa yau, saboda wasu matsaloli da su ka taso.

Ranar 21 ga watan da ya wuce, shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya naɗa Ismael Haniey na Hamas a matsayin saban Praminsita, bayan gagaramar nasara, da ƙungiyar ta samu, a zaɓen yan majalisun dokoki a watan janairu.

Ya zuwa yanzu, saban Praministann ya kasa girka gwamnati a dalili da riginginmun siyasa.

Idan ba a manta ba, ranar talata da ta wuce, yan majalisun dokokin Fatah, sun kauracewa Majalasar, bayan da yan Hamas masu rinjaye, su ka kada kuri´ar amincewa, da wata ayar doka da a cewar su, ta sabawa ka´idodji.

A nasa ɓangaren shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, na ci gaba da rokwan kasashen dunia, da su tallafawa Palestinu, da kuɗaɗe.

Wannan kira, ya biwo bayan barazanar da ƙasashe masu hannu da shuni su ka yi, ta katse duk wasu hulɗoɗi na agaji ga Hamas, da su ka ɗauka tamkar wata ƙungiyar yan ta´ada.