Taro a game da Mahhali a Nairobi | Labarai | DW | 15.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taro a game da Mahhali a Nairobi

Ministocin kula da mahhali daga ƙasashe daban-daban na dunia, na ci gaba da zaman taro a Nairobin Kenya.

Wannan gagaramintaro da ya samu halartar sakataren Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, ya maida alkibla a game da batun ɗumamar yanayi, da kuma matakan samun rangwame.

A jawabin da ya yayi Annan, ya danganta matsalolin gurɓacewar yanayi, tamkar wani makami mai guba, wanda ke hadasa ta´adi a dunia.

Duk da cewar MDD, na iya ƙoƙarin ta, wajen samar da hanyoyin ɓullowa matsalar, ƙasashen dunia ba su taka rawar da ya dace, da dama daga cikin su na nuna halayen ko in kulla, ta fannin aiwatar da yarjejeniyar Kioto, da ta tanadi yaƙi, da gurgusuwar hamada, da gurbatar yanayi.

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya tabarawa ƙasashe masu tasowa, ci gaba da ƙoƙarin don talafa masu, su yaƙi bila´in taɓarɓarewar mahhali.