Tarihin Thomas Sankara | Amsoshin takardunku | DW | 02.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Thomas Sankara

An haifi Thomas Sankara a ne a garin Yako na kasar Burkina Faso a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 1949.Mahaifansa 'yan kabilar nan ce ta Slimi-Mossi.

An haifi Thomas Sankara a ne a garin Yako na kasar Burkina Faso a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 1949. Mahaifansa 'yan kabilar nan ce ta Slimi-Mossi. Thomas ya fara karatunsa na Firamare ne a garin nan na Gaoua, daga bisani kuma ya tafi Bobo-Dioulasso gari na biyu mafi girma a Burkina Faso din domin yin karatunsa na gaba da sakandare.

Mahaifan Thomas Sankara dai sun so dan nasu ya zama limamin addinin Kirista to sai dai hakan ba ta samu ba don bayan kammala karatunsa na gaba da Firamare ya shiga aikin soja inda ya samu horo a matakai da dama. Ya dai shiga horonsa na soja na farko ne a shekara ta 1966. Lokacin da ya ke dan shekaru 20 da haihuwa ne kuma aka tura shi kasar Madagascar domin samun horo kuma a kasar ce ya yi karance-karance ciki kuwa har da litattafan shararraren marubucin nan Karl max.

Lokacin da ya kammala karbar horonsa a shekara ta 1972 dai ya ci karo da yakin da aka yi tsakanin kasarsa da kuma Mali a cikin shekarar 1974. Wannan yaki dai na daga cikin abubuwan da suka sanya Sankara ya shahara a wancan lokacin saboda irin jarumtar da ya nuna a lokacin da ya ke fagen daga. Bayan da kura ta lafa, a shekara ta 1976 aka nada shi kwamandan wata cibiya ta horas da sojin Burkina Faso a garin Po, kuma ita wannan shekara ce ya hada Blaise Compaore wanda shi ma kamar Sankara tsohon shugaban kasar ta Burkina ne.

A cikin shekarar 1981 dai an nada Sankara a matsayin sakataren da ke kula ma'aikatar yada labarai inda a wannan lokacin ya je taron farko na majalisar ministocin kasar a kan keke lamarin da jama'a da dama a kasar suka yi ta tsokaci a kai. To sai dai bai jima kan wannan matsayi ba don a shekara ta 1982 ya mika takardarsa ta murabus bisa dalilin da ya bada na hana mutane fadin albarkacin bakunansu.

Bayan da kasar ta Burkina Faso ta gamu da juyin mulki a shekarar 1982, an nada Sankara firaminista a watan Janairun 1983 sai dai hukumomin Faransa sun sauke shi bayan da wakilin gwamnatin kasar da ke kula da harkokin kasashen Afirka ya ziyarci kasar. Daga bisani kuma ma aka yi masa daurin talala da shi da shugaban mulkin sojin kasar na lokacin Manjo Doctor Jean-Baptiste Ouédraogo, lamarin da ya haifar da yamutsi a kasar baki daya.

To a cikin shekarar ta 1983 ne dai Thomas Sankara ya zama shugaban kasar Burkina Faso lokacin da ya ke da shekaru 33 da haihuwa bayan wani juyin mulki da Blaise Campaore ya shiya. Kasar Libya wadda a daidai wannan lokacin ke takun saka da kasar Faransa dai na daga cikin wanda suka taimaka wannan juyin mulki da ya dora sankara kan gadon mulki ya yi nasara.

Lokacin da ya shugabanci kasar dai, ya yi mulkin da ya baiwa al'ummar kasar 'yancin fadin albarkacin baki da yaki da cin hanci da samar da aiyyukan yi da tabbatar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da ilimi ga 'yan kasa gami da sanya idanu wajen ganin an yaki hamada a kasar ta hanyar samar da dazuka. Kuma lokacin da ya shekara daya a kan gadon mulki ne ya sauya tutar kasar da sauya mata suna daga Upper Volta zuwa Burkina Faso.

Al'ummar Burkina Faso dai a wancan lokacin sun yaba da irin salon shugbancin Thomas Sankara, lamarin da suke kallo a matsayin wata hanya ta maida kasar kan gaba a jerin takwarorinta to sai dai wannan fata nasu ya ci karo da cikas sakamakon hallaka shi da aka yi a wani juyin mulki wanda abokin aikinsa Blaise Campaore ya shirya a ranar 15 ga watan Oktoban shekara ta 1987. Bayan juyin mulki dai mai dakinsa Mariam da yaransa biyu sun arce daga kasar don tsira da ransu.

Bayan da kura ta lafa dai, Blaise Campaore ya dare kan kujerar shugabancin Burkina Faso inda ya jagoranci kasar har zuwa shekara ta 2014 da ta gabata lokacin da ya bar gadon mulki sakamakon jerin zanga-zanga da aka rika yi ta adawa da mulkinsa. A 'yan kwanakin da suka gabata ne dai aka bada sammacin kama Campaore ko ina ya ke a duniya don fuskantar shari'a bisa hannun da aka ce ya ke da shi wajen kashe Thomas Sankara.