Tarihin Mullah Omar shugaban kungiyar Taliban | Amsoshin takardunku | DW | 17.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Mullah Omar shugaban kungiyar Taliban

An haifi Mullah Omar tsakanin shekara ta 1950 zuwa ta 1961 a wani kauye mai suna Noori na cikin jihar Qandahar na kasar Afganistan.

Mullah Omar shugaban kungiyar Taliban sunanshi na ainahi shi ne Muhammad Umar bin Maulwi Ghulam Nabi Akhwand bin Mulla Muhammad Rasool Akhwand bin Mulla Muhammad Ayaz Akhwand.

Akwai sabani tsakanin marubuta a kan shearar aihuwarsa, amma dai dukkanninsu na cewa an haife shi ne tsakanin shekarara 1950 zuwa 1961 a wani kauye mai suna Noori cikin Jihar Qandahar a kasar Afganistan. Kuma tarihi ya nunar da cewa zuri’arsu tun daga kakanni da iyaye fitattun malamai .

A saurari cikakken shirin domin samun karin bayani

Sauti da bidiyo akan labarin