Tarihin Issa Hayatou | Amsoshin takardunku | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Issa Hayatou

Issa Hayatou ya zama shugaban wucin gadi na hukumar FIFA bayan dakatar da Sepp Blatter.

An haifi Issa Hayatou ranar 9 ga watan Agusta 1946 a garin Garwa na kasar Kameru inda yanzu yake da shekaru 69 a duniya. Hayatou ya rike mukamai daban-daban a hukumar wasan kasar ta Kameru da suka hada da shugaban hukumar wasanni ta kasa. Kuma tun ranar 10 ga watan Maris 1988 ya zama shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka.

Yanzu haka Issa Hayatou ke rike da mukamun shugaban wucin gadi na hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA, bayan dakatar da shugaban hukumar Sepp Blatter, bisa zargin cin hanci da rashawa.