Issa Hayatou ya zama shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka a ranar 10 ga watan Maris 1988, kuma dan gidan sarauta ne a Arewacin Kamaru
An haife shi a ranar 9 ga watan Agusta 1946 a garin Garoua na kasar Kamaru, inda ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban hukumar kwallon kafar kasar. Kuma a ranar 10 ga watan Maris 1988 ya zama shugaban hukumar FIFA na riko.