1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar Tarayyar Afirka a magance rikice-rikice

Antonio Cascais | Lateefa Mustapha Ja'afar SB
May 25, 2023

Shekaru 60 da suka gabata aka kafa kungiyar Hadin Kan Afirka OAU, kafin daga bisani a sauya mata suna zuwa kungiyar Tarayyar Afirka AU. An dai kafa kungiyar ne a ranar 25 ga watan Mayun shekara ta 1963.

https://p.dw.com/p/4Roty
Habasha shekaru 60 da kafa kungiyar Tarayyar Afirka
Tarayyar Afirka ta cika shekaru 60 da kafuwaHoto: Solomon Muchie/DW

Shekaru 60 da suka gabata aka kafa kungiyar Hadin Kan Afirka OAU, kafin daga bisani a sauya mata suna zuwa kungiyar Tarayyar Afirka AU. An dai kafa kungiyar ne a ranar 25 ga watan Mayun shekara ta 1963, a daidai lokacin da kasashen nahiyar Afirkan da dama, ba su jima da samun 'yancin cin gashin kansu daga Turawan mulkin mallaka. Sai dai masu sanya idanu na zargin kungiyar ta zma tamkar damisar takarda, wanda hakan ke da alaka da kimar da take da ita.

Karin Bayani: Kasuwanci mara shinge ya mamaye taron kolin Afirka

Habasha shekaru 60 da kafa kungiyar Tarayyar Afirka
Bikin cika shekaru 60 da kafa kungiyar Tarayyar AfirkaHoto: Solomon Muchie/DW

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam kamar Adriano Nuvunga shugaban wata kungiya mai zaman kanta a Mozambik wato Cibiyar Dimukuradiyya da Ci-gaba CDD, na ganin cewa kungiyar na zaman tamkar 'yar manuniya, ta samun 'yancin al'ummar Afirka da kuma fatan samun kyakkyawar makoma.  A wata hira da ya yi da tashar DW Nuvunga ya bayyana cewa, za a fahimci cikin jawaban kaddmar da kungiyar da shugabannin kasashen Afirkan suka yi ta gabatarwa. Ya kara da cewa ga misali a jawabinsa, shugaban kasar Ghana na farko Kwame Nkrumah ya bayyana cewa: "Tilas mu hada kanmu yanzu, ko kuma a shafe tarihinmu." Ya kamata a kawo karshen tsoma bakin kasashen ketare a harkokin Afirka, kana a samar da hadaddiyar Afirka da ke da bakin fada a ji a harkokin kasa da kasa. Sai dai shekaru 60 bayan kafa kungiyar Tarayyar Afirkan, har yanzu tana shan suka. Nuvunga na daga cikin wadanda ke sukan tsarin gudanar da kungiyar.

Ba dai Adriano Nuvunga ne kadai ke sukar kungiyar Tarayyar Afirkan dangane da batun rashin daukar mataki a kan rikice-rikice da yake-yaken da ake fama da su a kasashen Afirkan masu yawa ba, wannan wani abu ne da kungiyoyi masu zaman kansu da dama ke fada. Sai dai kuma shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz  ya yi wasu kalamai da suka sha bamban da na suka, a yayin ziyarar da ya kai cikin wannan wata na Mayu a kasashen Habasha da Kenya. Yayin wani taron manema labarai a birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar Habasha kana cibiyar kungiyar ta Tarayyar Afirka, Sholz ya bayyana fatan samar wa da AU din matsuguni cikin kungiyar G20 da aka kafa a 1999 da ta kunshi kasashe 19 masu karfin tattalin arziki da kuma kungiyar Tarayyar Turai.

Habasha shekaru 60 da kafa kungiyar Tarayyar Afirka
Bikin cika shekaru 60 da kafa kungiyar Tarayyar AfirkaHoto: Solomon Muchie/DW

Shin ko kungiyar ta AU za ta iya cimma babbar manufar kafata, wato hadin kai da tsaro da kuma zaman lafiya? Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya da sojojin Afirka ke ciki ba su taka wata rawar gani ba suma, a cewar kwararriya kan yankin arewacin Afirka daga cibiyar nazarin al'amuran Afirka ta Jamus da ke birnin Hamburg GIGA, Hager Ali a hirar da ta yi da tashar DW. A cewarta shirin wanzar da zaman lafiya da kungiyar Tarayyar Afirka ke ciki a Sudan da Mali, ba wai aikinsu su shawo kan matsalolin da ke da nasaba da shugabannin kasashen ba ne, sai dai domin su kare farar hula su kuma samar da hanoyiyn magance rikici.

A zahirin gaskiya za a iya cewa kungiyar Tarayyar Afirka tana da karfin iko ne akwai a rubuce, musamman idan aka yi la'akari da cewa tana wakiltar mutanen da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan 400. A yanzu dai, baki dayan kasashen nahiyar Afirka da al'ummomin kasa da kasa suka amince da su guda 55, na cikin wannan kungiya ta AU.