Tanzaniya za ta samu sabon tsarin mulki | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tanzaniya za ta samu sabon tsarin mulki

Ana takaddama kan zaben raba gardaman kundin tsarin mulkin Tanzaniya

Kasar Tanzaniya ta bayyana cewa cikin watan Afrilu mai zuwa za a gudanar da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Ministan shari'a na kasar Frederick Werema ya bayyana haka, abin da ya fusata 'yan adawa, wadanda suka kauracewa zaman rubuta sabon kundin tsarin mulkin. Idan sabon kundin tsarin mulkin ya wuce zai maye gurbin wanda ake amfani da shi tun shekarar 1977, lokacin da kasar da ke yankin gabashin Afirka take karkashin mulkin jam'iyya daya.

Babbar jam'iyyar adawa ta ce za ta nemi kotu ta hana zaben raba gardamar. Sabon kundin tsarin mulkin ya kara bai wa mata tacewa, kuma a shekara mai zuwa za a gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin kasar ta Tanzaniya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba