1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tanzaniya na jimamin mutuwar tsohon shugabanta

February 29, 2024

Ana jimamin mutuwar tsohon shugaban kasar Tanzaniya Ali Hassan Mwinyi wanda ya mutu yana da shekaru 98 bayan ya yi doguwar jinyar cutar kansar huhu a wani asibiti da ke birnin Dar es Salaam fadar gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/4d2to
Tansania Kamala Harris  Samia Suluhu Hassan
Hoto: Ericky Boniphace/AP/picture alliance

Ali Hassan Mwinyi wanda aka haifa a shekarar 1925, bayan ya yi gwagwarmaya a mukamai daban-daban ya dare kan gadon mulkin Tanzaniya a shekarar 1984 sannan kuma ya kasance shugaba na farko da ya saki mara ga kafa jam'uyyun masu ra'ayoyi mabambanta a kasar.

Babban abin da za a tuna a game da mariyayin shine rawar da ya taka wajen farfado da tattalin arzikin Tanzaniya tare da ceto kasar daga kangin talauci na shekaru masu yawa.

Tuni shugaban kasar Samia Suluhu Hassan ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai tare da sausauto tutar kasar kasa domin girmama marigayin da ake bayyanawa a matsayin gwarzon gwarzaye a kasar ta Tanzaniya da ke Gabashin Afrika.