Tanzaniya da Mozambik za su yaki ta′addanci | Labarai | DW | 24.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tanzaniya da Mozambik za su yaki ta'addanci

Kasashen Tanzaniya da Mozambique sun rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da ta'addanci a tsakaninsu.

 A karkashin yarjejeniyar Tanzaniya za ta mika wa Mozambique 'yan bindigar kasar 500 da ta kama bayan sun arce daga Mozambik din.  Shugaban rundunar 'yan sandan Tanzaniya Simon Sirro ya ce a yanzu sun amince su hada karfi wurin yaki da 'yan bindigar da ke yawo a tsakanin iyakar kasashen makwabtan juna.

A 'yan watannin nan dai 'yan bindiga na yankin Cabo Delgado mai arzikin Gas a Mozambik sun tsananta kai hare-haren da a yanzu suka yi naso zuwa kasar Tanzaniya.