Tambuwal da Masari sun lashe zaben gwamnoni | Labarai | DW | 12.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tambuwal da Masari sun lashe zaben gwamnoni

Sakamakon zaben gwamnoni ya nunar da cewar 'yan takara na jam'iyyar APC sun lashe jihohin Sokoto da Katsina da kaduna da Imo, yayin da PDP mai mulki ta lashe jihar Gombe.

An fara samun sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majlisar dokoki na jihohi da aka gudanar a Najeriya, inda ya zuwa jam’iyyar PDP da ke mulki ta samu kujerar gwamna guda daya a Gombe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya . Farfesa Saminu Adurahman Ibrahim na INEC ne ya ayyana gwamnan mai ci Ibrahim Hassan Dankwambo a matsayin wanda ya lashe zaben, gaban dan takarar APC wanda tuni ya amince da shna kaye.

Sai dai kuma jam'iyyar APC ta zababben shugaban kasar Najeriya muhammadu buhari ta na sa ran lashe kujerun gwamnoni a jihohi da dama musamman ma a arewacin kasar. Yanzu haka ma dai tsohon shugaban majalisar wakilan Nigeria, Aminu Bello Masari ya lashe zaben gwamna a jihar Katsina karkashin jam'iyyar APC. Shi ma dai kakakin majalisar na yanzu Aminu Waziri Tambuwal ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben gwamnan jihar Sokoto, gaban surikinsa Sanata Abdullah Wali na jam'iyyar PDP.

Shi ma tsohon ministan tarayyar Abuja Nasir el rufai ya lashe kujarar gwamna a kaduna karkashin inuwar jam'iyyar APC.A jihar Oyo da ke kudancin kasar kuwa, Sanata Abiola Ajimobi na APC ya samu damar yin tazarce a kujerar gwamnan jihar bayan da ya samu rinjaye kuri'u gaban tsofaffin gwamnonin jihar biyu watau Rashidi Ladoja da kuma Adebayo Alao-Akala na jam'iyyar Labour.