Tallafin karatu ga marasa galihu | Himma dai Matasa | DW | 15.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Tallafin karatu ga marasa galihu

A yunkurinta na ganin ilimi musamman ma na boko ya wadata, wata mata a Bauchi ta dukufa wajen koyar da mata da yara musamman ma marasa galihu da nufin ganin sun samu ilimi kamar kowa.

Wata malamar makaranta ta sadaukar da kanta wajen koyawa kananan yara marayu karatu. Baya ga wannan, matar na koyar da manyan mata da nufin ganin sun yaki jahilci. Galibin matan da suka ci moriyar wannan shiri ba su samu damar yin karatu ba saboda aure ko kuma rashin kudin da za a biya musu su yi karatun.

Ita dai wannan mata mai suna Bilkisu Abubakar Sambo mai makaranta ko cibiyar koyar da ilmi da akayi wa lakabi da suna ''Minal Learning Foundation'' ta kasa makarantar sashe-sashe har zuwa gida hudu da suka hada da na kananan yara da na 'yan mata matasa da kuma manyan mata masu koyon yaki da jahilci.

Wakilin DW da ke Bauchi Ado Abdullahi Hazzad ya samu zagawa makarantar inda ya shiga azuzuwa kana ya tarar da malamai na bada darasi ga dalibai. Duk da irin wannan yunkuri da ta yi, mai makaranta ta ce suna neman taimako daga gwamnatin da nufin ganin hakarsu ta kai ga cimma ruwa.