Tallafin ilimi a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 11.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Tallafin ilimi a Najeriya

A Jihar Katsina da ke Najeriya wani matashi ya tashi tsaye domin taimakon mutane a fannin ili ta hanyar gidan makaranta.

A Jihar katsina da ke Najeriya wani mai taimakon al'umma ya gina wata makarantar boko wadda ake kira "Islamic College" a wata unguwar talakawa dan saukaka wa yaransu. Ita dai wannan makaranta ta kunshi primary da secondary daga jihar ta katsina wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba ya aiko mana da karin bayani. Ita dai wannan makaranta an gina tane a unguwar kofar guga dake cikin garin Katsina Alh Usman Sarki shi ne ya samar da wannan makaranta yace duba da irin doguwar tafiyar da Daliban unguwar ke yi zuwa wasu makarantu.

Dogaro da kai na daga cikin abunda kullun ake fadi tashin ganin mutasa a Nigeria sun samu dan cigaban Al,umma hakanne yasa Usaman Sarki yace wannan makaranta ba'a barta a baya ba dan har sashin hiradda matasa sana'o'i a ware

Na samu halartar lokacin da aka bude wannan makaranta a unguwar kofar guga dake cikin garin na katsina inda Al,umma sukai taran gwarin dango dan nuna murna ganin an sauwake masu wato nisa tazo kusa kuma naji ta bakin kadan daga cikin iyayen yara.