1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta kwace ikon gundumomi 6 a Afghanistan

June 14, 2021

Rahotanni daga Afghanistan sun tabbatar da cewa mayakan Taliban sun kwace iko tare da fattatakar dakarun gwamnatin kasar daga gundumomi 6 a cikin sa'o'i 24.  

https://p.dw.com/p/3useY
Bildergalerie Truppenabzug Afghanistan | Befreiung Gefangener aus Taliban-Gefängnis
Hoto: Ajmal Kakar/Xinhua News Agency/picture alliance

Shugabanin yankunan sun tabbatar da cewa dakarun da suka dade suna aiki a gundunmomin ka iya kasance wa sun tsere ne don shiga wasu rundunonin yayin da suka bar makamansu da alburusan yaki. Sai dai kuma baya ga gundumomi 6 da kungiyar ta kwace iko, dakarun gwamnatin kasar sun kwato ikon gundumar Khan Abad daga hannun mayakan.

Rikici na kara rincabewa a kasar ta Afghanistan yayin da mayakan Taliban ke ci gaba da kwace ikon garuruwa tun bayan da Amirka da kungiyar NATO da sauran kasashe suka fara janye dakarunsu tun daga ranar 1 ga watan Mayun da ya gabata. Kawo yanzu dai a kalla gundumomi 23 ne ke karkashin ikon Taliban.