1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myanmar: Zargin cin zarafin bil Adama

Abdoulaye Mamane Amadou
August 5, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a sanya takunkumi na sayar da makamai ga rundunar sojin kasar Myanmar da kuma 'yan kasuwar da ke hulda da ita saboda zargin da ake musu na taimakawa wajen cin zarafin al'umma.

https://p.dw.com/p/3NLPq
Myanmar Grenzpolizei
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Htusan

Wani rahoto da wani kwamitin bincike na majalisar da ya yi aiki a Myanmar din ya fidda a wannan Litinin din ya nuna yadda wasu 'yan kasuwa da harkokinsu da rundunar sojin ta Myanmar suka shiga ake dama wa da su wajen cin zarafin 'yan kasar da ma bada gudumawa ta kudi wajen an fidda musulmi 'yan Rohingya da jihar nan ta Rakhine.

Gabannin fitar wannan rahoton dai, Majalisar ta Dinkin Duniya ta bada shawarar bicnikar shugabannin wasu kamfanoni biyu da ke da alaka da rundunar sojan kasar saboda zargin da ake musu na hannu a kisan kiyashi da keta alfarmar dan Adam da am laifukan yaki.