1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun sakar Amirka da Iran na karuwa

Yusuf Bala Nayaya
June 14, 2019

Daular Larabawa ta Dubai ta bayyana a wannan Juma'a cewa kai tagwayen hare-hare kan jirage na dakon mai a yankin tekun mashigar Oman babbar barazana ce, abin da ya sa Amirka tsoma baki.

https://p.dw.com/p/3KTTf
Golf von Oman - Schiffexplosion
Hoto: ISNA

Ministan harkokin wajen Dubai Anwar Gargash, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kai harin kan jiragen dakon mai abu ne mai tada hankali da ka iya harzuka lamura. Har ila yau Gargash ya yi Allah wadai da harin makami mai linzami da 'yan tawayen Yemen suka kai, harin da ya yi sanadi na raunata fararen hula 26 a filin jiragen sama da ke Kudu maso Yammacin Saudiyya. Gargash ya ce halin da ake ciki abu ne da ke bukatar sanya bakin kasa da kasa.

Amirka dai ta nuna Iran da cewa ita ke da hannu a harin jiragen. Sai dai Mohammad Javad Zarif ministan harkokin wajen Iran ya ce Amirka shishshigi ne ta kai ga cewa Iran ta yi wannan aika-aika.