Takun saka tsakanin Saudiyya da Iran | Siyasa | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takun saka tsakanin Saudiyya da Iran

A ranar Lahadi ne rushewar dangantaka tsakanin Iran da Saudi Arabiya ta kai kololuwarta bayan da Saudiyya katse dangantaka tsakanin ta da Iran.

Sabani a tsakanin kasashen biyu na yankin Gulf, wato Iran da Saudi Arabiya ba shi ne na farko ba a tarihinsu. Bayan banbancin akida, kasashen biyu sun kuma dade suna gwagwarmayar neman karfin iko a wannan yanki. Mafi rinjayen al'ummar Saudi Arabiya dai Wahabiyyawa ne masu bin tafarkin Sunna, yayin da 'yan Shia suka fi yawa a Iran. A shekara ta 1987, dangantaka ta yi tsami tsananinsu har ta kai kusan a tsunke ta gaba daya, lokacin da mahajjatan Iran kimanin 275 suka mutu batun da ya haifar da zanga-zanga mai karfi a Tehran.

Saudi-Arabien König Salman

Sarki Salam da gwamnatinsa sun zargi Iran da hannu a kone ofishin jakadancinsu da ke Iran.Saudi Arabiya dai a wannan karo ce ta dauki matakin kawo karshen dangantakar ta diplomasiya tsakanin kasashen biyu bayan da ta yi zargin cewar hukumomin Teheran ne suka sanya masu zanga-zangar ranar Lahadi suka je ofishin jakadancinta da ke kasar inda daga bisani abin ya jawo kone wajen baki daya. Sai dai Iran din ta musanta hakan.

Baya ga banbancin Sunni da Shia da ke tsakanin kasashen na Saudi Arabiya da Iran, Saudiyya din na zargin Tehran da laifin goyon bayan aiyukan tarzoma a yankin, abin da ke neman mamaye garuruwan kasar ta Saudi. Shugabannin na Saudi Arabiya sun zargi tsohon shugabgan Iran Mahmoud Ahmeninejd da laifin neman fadada ikon kasar a yankin Gulf ta hanyar karfafa matsayin 'yan Shia har ma a Saudi Arabiya da kuma neman hana zaman lafiya.

New York UN- Rede Hassan Rohani Iran

Shugaba Hassan Rouhani ya ce kisan da aka yi wa Nimr al-Nimr keta alfarmasa ce ta bil Adama.

A daura da wannan masana a nasu bangaren an cewar Saudiyya na da buri na ganin an maida Iran saniyar ware, yayin da kasashen Larabawa da ke bin tafarkin Shi'a ke cigaba da nuna goyon bayansu ga Iran. Kakakin 'yan tawayen Huthi a Yemen alal misali ya gargadi sarakunan Saudi Arabiyya da cewa bada izinin kashe jagoran 'yan Shia a kasar Nimr al-Nimr wata alama ce ta kawo karshen gidan sarautar saboda Saudiyya din ta aikata laifin da shi ne mafi muni a tarihinta.

Sauti da bidiyo akan labarin