Takaicin MDD kan rikicin Siriya | Labarai | DW | 29.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaicin MDD kan rikicin Siriya

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriya ya bayyana cewar, kada a yi gaggawar shirya wani taron sulhu a birnin Geneva, ba tare da bangarorin sun shirya ba.

Staffan de Mistura ya fada wa Kwamitin Sulhu cewar, fatan Majalisar Dinkin Duniya shi ne, lokacin da Siriyawan za su bayyana a wurin taron, suna da kyakkyawan guzuri dangane da makomar kasarsu a siyasance, musamman yadda za a warware rikicin.

A cewarsa muhimmin abun da aka cimma a taron sulhu tsakanin manyan kasashe a watan Yunin 2012, shi ne kafa gwamnatin rikon kwarya mai cikakken iko. Hakan shi ne tubali, kafin a gudanar da zabe, wanda zai bukaci shugaba Bashar al Assad ya mika mulki a wani lokacin da ba a zartar ba.

Babban sakataren MDD Ban Ki moon, ya fada wa Kwamitin Sulhun cewar, rikicin na Siriya da ya dauki sama da shekaru yana gudana, wanda ya lashe rayukan mutane a kalla dubu 250, alamu ne na gazawar al'ummomin kasa da kasa saboda rarrabuwar kawuna da ke tsakaninsu a kan rikicin.