Takaddamar yankin Kurdawa na Iraki | Labarai | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddamar yankin Kurdawa na Iraki

Wata kotu a birnin Bagadaza na Iraki ta ba da umurnin cafke shugaban hukumar zabe na yankin Kurdawa da matamankansa guda biyu wadanda suka kula da shirya zaben raba gardama na ballewar yankin da aka yi.

Wani babban jami'n kotun kolli na Irakin ya ce wadanda suka shirya zaben sun taka doka, bayan da babbar kotun ta dakatar da zaben gabanin ma a yi shi a cikin watan Satumbar da ya gabata. Makonnin biyu dai da yin zaben raba gardamar na yankin Kudawan wanda ya samu nasara har yanzu ana kai ruwa rana tsakanin hukumomin Bagadaza da na Erbil  cibiyar yankin na Kurdawa.