1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Trump da jaridar New York Times

Abdul-raheem Hassan
September 6, 2018

Jaridar ta wallafa sharhi da wani jami'in gwamnatin Amirka ya soki salon shugabancin Trump, tare da yin barazanar soke wasu manufofin gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/34PGA
Ohio Donald Trump Rede vor Anhängerschaft
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Minchillo

Marubucin da aka boye sunansa ya ce shugabancin Trump ba shi da alkibla, kana ya ce zai jefa Amirka cikin wani yanayi na rashin tabbas a idanun duniya. Sharhin ya yaba da wasu fannoni da Amirkar ta samu cigaba, amma ya ce akwai wasu manyan jami'an gwamnatin da ke aiki tukuru wajen rusa manyan akidojin gwmnatin.

Sai dai a martanin da shugaban ya mayar a shafinsa na Twitter, ya ce marubucin rago ne wanda ke tsoron bayyana kansa kana shugaban ya bayyana sharhin a matsayin cin fuska da cin amanar kasa. Trump ya bukacin jaridar New York Times din da ta gaggauta bayyana sunan jami'in da ya rubuta sharhin domin ya fuskanci hukunci.