1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Sudan ya ja hankalin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala SB
April 19, 2019

Yawancin jaridun na Jamus sun yi sharhinsu ne kan ci gaba da zanga-zangar da jama'a ke yi a kan sojoji a Sudan bayan kifar da gwamnati tsohon Shugaba Omar al Bashir.

https://p.dw.com/p/3H5C5
Sudan Protest vor Militärhauptquartier in Khartum
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

 

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta wanda ta yi wa taken kungiyar Tarayyar Afirka ta bai wa Sudan wa'adi, rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan adawa da kuma tasa keyar tsohon Shugaba Omar al Bashir.

Jaridar ta ce a birnin Khartoum 'yan zanga-zanga sun ci gaba da nuna turjiya ba kakkautawa kan sojoji bayan da suka yi kokarin kawar da su daga inda suke zaman dirshan a kofar hedikwatar sojojin. Kungiyar kwararrun ta Sudan wadda ke jagorantar zanga-zangar ta yi kira ga jama'a su zauna daram su kare gwagwarmayar juyin-juya halin.

Sudan Protest vor Militärhauptquartier in Khartum
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Sai dai kuma kawunan 'yan zanga-zangar sun rarrabu inda wasu jam'iyyu ke tunanin kafa gwamnatin wucin gadi da sojoji, sun amince su zauna a tattauna sai dai sun ce ba za su saki mukaman ministocin cikin gida da na tsaro ba kamar yadda sojojin suke bukata. A waje guda kuma kungiyar Tarayyar Afirka a wani mataki na ba sabon ba, ta yi barazanar korar Sudan daga ciki idan kasar ba ta koma kan tafarkin dimukuradiyya cikin makonni biyu ba.

A daya bangaren kuma babu tabbas kan makomar tsohon Shugaba Omar al Bashir mai shekaru 75 a duniya wanda kotun shari'ar manyan laifuka da ke birnin Hague ta ba da sammacin kama shi tun shekarar 2010 bisa ta'asar kisan jama'a a Darfur.

Wasu dai na ganin cewa babu wata hujja da masu zanga-zangar za su ci gaba da nuna rashin yarda da sojoji bayan babban hafsan soji kuma ministan tsaro Awad bin Auf da suka ce ba su yarda da shi ba ya yi murabus aka nada Abdul Fattah Burhan a matsayin shugaban rikon kwarya na majalisar soji. Hatta shugaban hukumar leken asiri Abadallah Gusch shi ma ya yi murabus. Sannan an nada Mohammed Hamdan Daglo dan uwa ga wani jigon 'yan kabilar Darfur a matsayin mataimakin Burhan an kuma kame manyan jagororin gwamnatin da ta shude duka dai don kwantar da hankalin 'yan zanga-.zangar amma lamarin ya faskara.

Sudan Unruhen Proteste in Khartum Kober Gefängnis
Hoto: Getty Images/AFP

Ita kuwa jaridar Die Zeit a sharhinta mai taken shin Sudan tana da damar samun cikakken 'yanci bayan kawar da shugabanta na kama karya kuma me zai faru a gaba?

Jaridar ta ce dubban jama'a sun yi ta murna da shewa da raye-raye a kan tituna, babu wanda ya yi tsammanin kawo karshen mulkin Omar al Bashir wanda ya shafe shekaru 30 a karagar mulki. Sun dade suna mulki shi da tsohon Shugaba Hosni Mubarak na Masar.

Jaridar ta ce lokacin da sojoji suka karbi mulki bayan kawar da Mubarak masu fafutuka sun yi gargadin cewa ba ta sauya zane ba domin kuwa mulki na nan a hannun mutane guda, a karshen 'yan fafutuka suna nan yau a gidan yari yayin da wasu suka yi gudun hijira wadanda suka zauna kuma an hana musu bakin magana karkashin sabon salon kama karya a Masar.

Daga cikin shugabannin yankin, Albashir shi ya fi wayo da dabara wajen tsallake siradi da dama walau na zanga-zanga ko na takunkumi cikinikayya da kuma barazana daga Amirka ko kotun duniya ta ICC.

Amma tambayar ita ce me ya kawo faduwar al Bashir a yanzu? A wannan karon dai zanga-zangar ta karfi kuma ta bazu a ko'ina a fadin kasar. Lamarin da ya faro da dan karamin bore kan tsadar burodi a watan Disamba na bara ya rikide zuwa gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati. Sassan al'umma, 'yan kasuwa da likitoci da dalibai da manoma da makiyaya, jama'a maza da mata Musulmi da Kirista da wadanda b asu da addini duk sun shiga zanga-zangar ta lumana ba tare da tashin hankali ba.

Sudan Unruhen Proteste in Khartum
Hoto: Reuters

Jami'an tsaro sun so su yi amfani da karfi inda suka bude wuta da ya yi sanadiyar mutuwar wasu 'yan zanga-zangar, daga baya aka sami baraka a tsakanin jami'an tsaron. Matasan sojoji sun tausayawa 'yan zanga-zangar.

Jaridar ta kara da cewa al Bashir ya kwan da sanin cewa soja ba shi da tabbas, sau biyu a baya a shekarar 1964 da kuma 1985 ana kawo karshen gwamnati bayan sojoji sun goyi bayan 'yan zanga-zanga a saboda haka al Bashir ya yi kokarin karawa wasu sojojin girma domin toshe musu baki.

To amma a karshe sun ba da shi cikin ruwan sanyi dama kuma an fara hango karshen mulkinsa tun 'yan shekaru da suka gabata.