1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Assasa takunkumin Amirka kan Iran

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
August 6, 2018

Amirka ta sake jaddada kudirinta na mayar da takunkuman karya tattalin arzikin da ta kakabawa Iran a Talatar wannan mako da muke ciki.

https://p.dw.com/p/32gt4
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Iran Hassan RohaniHoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Cikin watan Mayun da ya gabata ne dai Amirkan ta tsame hannunta daga cikin yarjejeniyar da kasashe shida masu fada a ji a duniya ciki kuwa har da ita Amirkan suka sanya hannu tare da Iran, kan batun makamashin nukiliyar kasar ta Iran, tare da shan alwashin maido da takunkuman karya tattalin arziki da a baya Amirkan ta kakabawa Iran din kuma aka cire ko kuma sassauta wasu daga ciki bayan cimma yarjejeniyar.

A wannan Litinin din ake sa ran shugaban kasar Iran Hassan Rohani zai yi jawabi a gidan talabijin din kasar dangane da matakan kariya da Tehran za ta dauka. Ana kuma sa ran zai sanar da matsayarsa dangane da tayin tattaunawa da shugaban Amirkan Donald Trump ya yi wa Tehran din. A cewar Pompeo za a iya samun mafita a takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu.