1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Amrka da Iran na kara kamari

Abdourahamane Hassane
July 19, 2019

Iran ta musunta ikirarin da Shugaban Amirka Donald Trump ya yi cewar wani jirgin ruwa na yaki na Amirka ya kakapo wani jirgin Iran marasa matuki.

https://p.dw.com/p/3MLLD
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Kamfanin dilancin labarai na Iran Tasnim ya ambato kakakin rundunar sojojin Iran din Janar Abdolfazi Sekarchi yana mai cewar dukkanin jiragensu mara matuka da suka tura shawagi  a mashingin Ormuz da ke a yankin Gulf sun dawo lami lafiya. Mashigin na Detroit Ormuz wanda a nan kusan kishi daya na man fetir da ake jigilarsa a duniYa ya ke bi, ya kasance wani abin rikici tsakanin Amirka da Iran wanda kowane ke kara jige sojojinsa a gewayen mashigin.