Taimako daga likitoci | Sauyi a Afirka | DW | 03.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Taimako daga likitoci

A Jamhuriyar Nijar wadansu matasa kwararrun likitoci ne da ke aiki a asibitoci daban-daban suka kafa wata kungiya da zummar kawo dauki ga yan kasar masu karamin karfi.

Matasan Kwararrun likitocin dai kan yi mai taro mai sisi ne don sayen magani kafin su yanke hukumcin zabar wani kauye da ke iya zama mafi tsananin bukata don kai daukin tare da baiwa jama'ar magani kyauta bayan binciken lafiyar su ,

Dr Abdel Kader Andia na daya daga cikin matasan likitocin da suka shirya gangamin yau shekaru uku ke nan suna aikin nan kuma babar manufar ita ce kusanto ga jama'a musamman wadanda ba su da damar ganin likita kwararru.

Malam Hamani Abdoulaye daya ne daga cikin masu fada aji na garin ya bayyana matukar farin cikin ganin matasan likitocin. Tuni wasu matasan kasar suka bayyana gamsuwa da matakin da kwararrun matasan likitocin suka dauka tare da bayyana fatar ganin tsarin ya dore don taimakon masu karamin karfi.

A tsawon wuni daya na gangamin akalla mutune 300 ne mata da yara da ma tsofaffin gari da na makwafta suka karbi magani bayan binciken lafiyarsu a yayin gangamin matasan lamarin ya sha san barka da kasancewa a bin misali ga wasu matasa na kasar.