Taho mu gamar Falasdinawa da sojan Isra′ila | Labarai | DW | 15.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taho mu gamar Falasdinawa da sojan Isra'ila

An yi taho mu gama tsakanin dakarun sojan Isra'ila da daruruwan Falasdinawa masu zanga-zanga a iyakar da ke gabashin Zirin Gaza da Isra'ila.

Wannan rikici na zuwa a yayin gangami na tunawa da ranar Nakba da suke kira ranar "tashin hankali" kamar yadda Falasdinawa ke bayyana ranar ta tuni da lokacin da aka kirkiri kasar ta Isra'ila a shekarar 1948. Suna tunawa da wannan rana ne dai a irin wannan lokaci duk watan Mayu inda suke gangami na zanga-zanga da a lokuta da dama ke rikidewa zuwa tashin hankali.

Jami'an lafiya a bangaren na Falasdinawa sun ce wasu mutane sun samu raunika a har gitsin yayin da wani da ya sheda lamarin ya ce ya ga yadda sojan na Isra'ila ke amfani da ruwan kwata suna fesa wa Falasdinawan da harba masu hayaki me sa hawaye da ma amfani da harsashin roba. Mai magana da yawun sojan na Isra'ila ta bayyana cewa akwai kimanin masu zanga-zanga 1200  wadanda ke tunkarar iyaka da Isra'ila soja na amfani da dabaru na tarwatsa zanga-zanga suna korarsu.